4 Yuni 2015 - 08:58
Gobara ta kashe mutane 70 Ghana

Rahotanni daga Accra, babban birnin kasar Ghana sun ce a kalla mutane 70 ne suka rasa rayukansu sannan kuma wasu da dama suka jikkata sakamakon wata gobara da ta tashi a wani gidan mai, a ranar Laraba da daddare.

Al'amarin dai ya faru ne a lokacin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya, a inda mutane suka nemi mafaka a gidan man, kwatsam sai gobara ta tashi abin da yayi sanadiyar mutuwar mutanen.

Sai dai kuma bayanai na cewa adadin wadanda suka rasa rayukan nasu na iya karuwa bisa la'akari da girman gobarar.

Hukumomin kasar dai sun tabbatar da afkuwar al'amarin.ABNA